Receive More Updates


SMS: Send FOLLOW R_E_T_B To 40404 For Free - EMAIL: REALITYTECHBLOGS@GMAIL.COM
prexblog notifications

» » Kadan Daga Cikin Bayani Akan Mutuwa

Thursday, 28 December 2017

Kadan Daga Cikin Bayani Akan MutuwaMUTUWA ITACE BABBAN WA'AZI KUMA AYA GA DUKKANIN MAI HANKALI DA TUNANI, KUMA ITACE ABU NA FARKO WANDA IDAN MUTUM MAI IMANI YA TUNO TA KUMA YA TABBATAR SAI YA DANDANI DACINTA YAKE RAGE BURI A RAYUWA.

MUTUWA ITACE TAZAMA DOLE GA DUKKAN MAI RAI SAIYA DANDANA DACINTA  KO YANASO KO BAYASO BA TARE DA SANIN LOKACIN DA ZATA ZOBA BATA KWANKWASA KOFA KO SANAR DA LOKACIN ZUWAN MAI AJALI KUMA ITACE DUKKAN MASU IMANI BASA IYA BACCI SAI SUN TUNATA.

MUTUWA ITACE BAKUWAR DA BATA SALLAMA, BATA FADIN ZUWANTA, SAI DAI KAWAI TAZO TA TAFI DA MUTUM BAGTATAN AKAN AIKINSA NA ALKHAIRI KO SHARRI.
MUTUWA ITACE KOMAI KUDINKA A DUNIYA KUMA KOMAI MULKINKA IDAN LOKACIN ZUWANTA GAREKA YAYI SAI TAZO TA TAFI DA KAI DAGA KAI SAI HALINKA BA KUDI KUMA BABU MULKI, DAGA KAI SAI HALINKA.

DAG KARSHE

TABBAS DUK LOKACIN DANA TUNA DA CEWAR WATAN WATA RANA FA ZAM MUTU, KUMA BANSAN RANA KO LOKACI DA MUTUWAN ZATA ZOMIN BA, BANSAN WURIN KO A HALIN DA MUTUWA ZATA RISKENI BA, WANNAN ABU YANA MATUKAR TADAMIN HANKALI DON HAKA MUNA FATAN ALLAH KASA MUYI KYAKWAN KARSHE, MU CIKA DA KYAU DA IMANI, KUMA ALLAH KASA ALJANNAH FIDDAUSI ITACE MAKOMA TA KARSHE A GAREMU BAKI DAYA BADAN HALINMU BA SAI DAN YAFIYANKA DA RAHAMARKA YA ALLAH.
No comments:

Post a Comment

Realitytech