Receive More Updates


SMS: Send FOLLOW R_E_T_B To 40404 For Free - EMAIL: REALITYTECHBLOGS@GMAIL.COM
prexblog notifications

» » MATA IRI BAKWAI KARKU AURE SU

Wednesday, 27 December 2017

MATA IRI BAKWAI KARKU AURE SU1-Al-Annaanah: Itace mace mai yawan karyar ciwon kai ko kuma ciwon wani abin daban, Alhali kuma karya take yi, Babu Abinda ke damunta,
To tun kafin ka Aureta Idan ka gane ta da wannan halaye na karyar ciwo don cimma wani manufarta to kayi hattara.

2-Al-Mannaanah: Mace mai yawan gori ga mijinta musamman idan tayi masa kyauta, ko tayi wani aikin dashi ya sata, wanda za kaga tana yawan cewa
"na yi maka kaza da kaza ai" haka ma ranar nan nayi maka kaza ai"
To idan ka gane ta da haka to kayi mata Nasiha idan taki dainawa to kayi hattara.

3-Al-Hannaanah: mace mai yabon 'ya'yan tsohon mijinta a gaban sabon mijinta wanda za kaji tana cewa "ai yaran tsohon mijinta sun fi naka yaran" da dai sauran cin fuska, to ka hakura da ita yafi alheri.

4-Kai' Atul Qafaa: Macen da take da "bad record" wanda ya kai ga duk jama'a suna ganinta da mummunan hali da rashin kima to kayi hattara da auren irin wannan mata.

5-Al-Haddaaqah: Macen da idan taga wani abu wanda take so sai ta tilasta ta takurawa mijinta yasai mata kota halin kaka itadai yasai mata. Yawanci ana gane su saboda sune tin kafinka Auro su zaka ga tana damunka da sai ka sai mata kaza ko sai ka bata kudin anko da dai sauransu,to kayi hattara da auren irin su.

6-Al-Shaddaaqah: Macen da take da yawan surutu, ta yadda bata rike sirrin mijinta, Ana gane irinsu idan suna Yan Mata,
domin sune da zaran kayi sirri dasu za suje suna fadawa kawayensu.

7-Al-Barraaqah: Mace mai yawan bata lokacinta a rayuwa wajen yin kwalliya,wanda zata dauki tsawon awanni tana shafe-shafe kamar zata canza halittar ta.
Kayi hattara da Auren irin wadannan Inji Sheikh Uthaymeen.

A Duba littafinnan mai suna "A Concise Manual OfMarriage By Shaikh Muhammad Ibn Uthaymeen".
Bawai Aurensu Haramun bane, Shaikh Uthaymeen Yana baka shawara ne akansu, daka auri irinsu
Gamma ka hakura yafi maka Alheri.
No comments:

Post a Comment

Realitytech